Wasu kulob a Nigeria na jiran samun garabar su ta wasa

Nigeria CAF Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nigeria CAF

Kuloblikan Nigeria na Enyimba da Sunshine Stars da Kaduna United sun ce har yanzu ba su samu garabasar shigar su wasannin kasa da kasa na shekarar 2011 ba.

Enyimba da Sunshine sun kai wasan kusa da na karshe a wasannin league na zakarun Afurka da kuma na zakarun nahiyoyi.

To amma dukkanin kuloblikan guda biyu hadi da Kaduna United sun kasa kaiwa ko ina fagen wasan share fage na rukunin su a gasar zakarun nahiyoyi, kuma har yanzu ba kai ga biyan su kudaden su ba, watanni biyar bayan kammala wasannin.

To sai dai, a na ta bangare hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afirka CAF ta ce kokari ta ke ta tabbatar da cewa kudaden sun kai zuwa ga wadanda ya kamata.

Shugaban kulob din Sunshine Stars Mike Idoko ya bayyana cewa sun aika da wasikar korafin su ga hukumar ta CAF ta hannun hukumar kwallon kafar Nigeria NFF, amma har yanzu shiru.

Karin bayani