Toure da Balotelli sun musanta yin fada a Manchester City

Yaya Toure Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yaya Toure

Dan wasan gaba na Manchester City Yaya Toure ya ce, rade radin da ake yadawa cewa ya yi fada da abokin wasan sa Mario Balotelli, ya bata masa rai, don ba gaskiya ba ne.

Rahotanni dai na nuna cewa yan wasan biyu sun baiwa hammata iska a dakin canza kaya a lokacin wasan su da Sunderland inda aka tashi ukku da ukku, wanda ya kai ga City ta sake yin kasa ga Manchester United.

Toure ya ce, ba gaskiya ba ne, ni dan wasan kwallon kafa ne, ba dan dambe ba.

Ya kara da cewa, mutane ba su san alakar mu da Mario ba, shi ba aboki na ba ne, dan uwa na ne.

Manchester City dai ta rikito a wasan Premier bayan shafe watanni shidda tana na daya, inda Manchester United ta tsere ma ta da maki biyar.

Karin bayani