Babu wani korafi kan gasar F1 a Bahrain

Bahrain Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Gasar tseren motoci ta Bahrain Grand Prix

Shugaban kula da gasar tseren motoci ta F1 Bernie Ecclestone ya ce kawo yanzu babu wata kungiya da ta nuna damuwa kan gasar da za a gudanar a kasar Bahrain, amma ya ce mai yiwuwa ba za a ci gaba da yin gasar a nan gaba ba.

Akwai rahotannin da ke nuna cewa wasu kungiyoyi sun nuna shakku kan halartar gasar saboda rikicin siyasar da ake fama da shi a kasar.

Ecclestone ya shaida wa wakilin BBC Dan Roan cewa: "Babu wata kungiya da ta gabatar min da korafi - haka nima ban yi korafi ba."

Dangane da batun ci gaba da gasar a Bahrain kuwa, ya kara da cewa: "Mai yiwuwa ba za mu sake kulla yarjejeniyar ba. Za mu duba mu gani."

An dage gasar da aka shirya gudanarwa bara bayan da kungiyoyin kare hakkin bil'adama suka nemi shugabannin F1 da su yi nazari kan ko za a gudanar da gasar ta bana.

Tsohon zakaran gasar ta duniya Damon Hill ya amince cewa ya kamata a sake duba matsayin gasar, sai dai Ecclestone ya nace cewa babu wani korafin tsaro daga kungiyoyi ko kuma jami'ai.