Ghana ta nada Appiah a matsayin kocin Black Stars

Tawagar Ghana Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tawagar Ghana ta fuskanci koma-baya a 'yan kwanakin nan

Hukumar kula da kwallon kafa ta kasar Ghana ta nada James Kwesi Appiah a matsayin sabon kocin kungiyar kwallon kasar ta Black Stars.

Appiah, wanda shi ne mataimamkin kocin Black Stars tun shekara ta 2008, ya maye gurbin dan kasar Serbia Goran Stevanovic, wanda aka kora a watan da ya gabata, bayan da kasar ta kasa kaiwa wasan karshe na gasar cin kofin kasashen Afrika.

Tsohon dan wasan na kasar ta Ghana zai gana da kwamitin gudanarwa na Hukumar kwallon kasar a ranar Talata domin kammala yarjejeniyar.

Appiah shi ne ya jagoranci Ghana ta samu nasara a wasan motsa jiki na 'yan kasa da shekaru 23 na kasashen Afrika.

Da farko an yi hasashen za a nada tsohon dan wasan Faransa kuma haifaffen kasar ta Ghana Marcel Desailly a matsayin sabon kocin.

Kalubalen farko da ke gaban Appiah, shi ne na shirya wa gasar share fagen shiga gasar cin kofin duniya ta 2014 da za su fafata da Lesotho a watan Juni.

Karin bayani