Burin Redknapp game da Tottenham

Redknapp Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Harry Redknapp da kungiyarsa ta Tottenham na cikin tsaka mai wuya

Kocin Tottenham Harry Redknapp ya ce wajibi ne kungiyarta sa ta lashe wasanni biyar din da suka rage musu idan har suna son kasancewa a jerin kungiyoyi hudu na saman teburin Premier.

A yanzu tawagar ta Redknapp su ne na hudu a tebur bayan da suka sha kashi a hannun Norwich sai dai Newcastle na biye musu ne kawai da tazarar kwallaye, yayin da ita ma Chelsea ke kokarin cimmu su.

"Muna bukatar mu lashe dukkannin wasanninmu biyar," a cewar Redknapp.

"A yanzu dama ce ga kungiyar da ke da wasanni masu sauki don haka wajibi ne mu yi amfani da damar da muke da ita."

Tottenham za ta kara da Chelsea a wasan kusa da karshe na gasar cin kofin FA ranar Lahadi, kuma za ta kara da kungiyoyin QPR, Blackburn, Bolton da kuma Aston Villa, wadanda dukka ke kokarin kare matsayinsu a kakar bana ta Premier.

Redknapp yana sane cewa wajibi ne su kara kaimi bayan kashin da suka sha a hannun Norwich a filin wasa na White Hart Lane wanda ya nuna cewa Spurs ta lashe wasa daya ne kacal a cikin takwas da ta buga a baya-bayan nan.

Karin bayani