Abidal na murmurewa - In ji Rosell

Eric Abidal Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Abidal yana taka rawa sosai a Barcelona

Shugaban kulob din Barcelona Sandro Rosell ya ce dan wasan kulob din Eroc Abidal na murmurewa kwana guda bayan tiyatar da aka yi masa a hantarsa.

Yace duka Abidal da kuma dan uwansa suan samun samun sauki amma ba zan bayar da wani karin bayani ba kamar yadda iyalinsa suka nema.

Abidal mai shekaru 32, an sa masa hantar dan uwansa Gerard ne a wata tiyata da aka yi masa wacce ta dauki tsawon sa'o'i tara ranar Talata.

Shi ma mai horar da 'yan wasan Barcelona, Pep Guardiola, ya ce ya sadaukar da nasarar da suka samu ta lallasa kungiyar Getafe da ci 4-0 ranar Talata ga Eric Abidal.

Tsawon sa'o'i goma likitoci suka yi suna yiwa dan wasan na kasar Faransa, aikin dashen hanta, yayin da magoya bayan Barcelonan suke masa fatan samun lafiya inda a dai dai minti 22 da fara wasan nasu da Getafe, suka barke da sowa ta nuna goyon bayansu ga dan wasan.

Guardiola, ya shaida wa manema labarai bayan wasan cewa ''ina son in sadaukar da wannan nasara ga Abidal da dan uwansa Gerard, wanda ya bada hantar da aka dasa masa''

Za mu ga yadda zai murmure zuwa sati mai zuwa. Muna godiya ga likitocin da suka yi masa tiyatar, kuma mun yi imanin cewa zai ci gaba da murmurewa saboda mutum ne mai juriya da karfin hali.

Wannan nasara da Barcelonan ta samu ta bada kwarya kwaryar damar matsowa gab da Real Madrid da maki daya kacal a tsakaninsu, kafin wasan da Real din za ta yi da Atletico Madrid ranar Laraba.