Muna gab da lashe gasar La liga - In ji Ronaldo

Cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Maki hudu ne ya raba tsakanin Madrid da Barcelona

Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya ce kulob din na gab da lashe gasar La liga, sannan ya yabawa abokan kwallonsa kan nasarar da ya samu ta zira kwallaye uku.

Sau bakwai kenan Ronaldo ya zira kwallaye uku a kakar wasa ta bana a La Liga, inda kawo yanzu ya zira kwallaye 52 a kakar bana, 40 a gasar La Liga.

Nasarar ta sanya Madrid ta kasance a saman tebur da tazarar maki hudu a gaban Barcelona, kuma Ronaldo na ganin sun kama hanyar lashe gasar.

"Akwai sauran aiki, sai dai mun kusa lashe La liga. Ni ban saba fuskantar rashin nasara ba," kamar yadda Ronaldo ya shaida wa manema labarai.

"Mun fuskanci matsin lamba saboda Barcelona ta riga ta lashe wasanta, amma yanzu muna da tazarar maki hudu."

A yanzu Cristiano Ronaldo ya zira kwallaye 52 a kakar bana bayan kwallaye ukun da ya zira ranar Laraba, sannan ya zamo dan wasa na farko da ya zira kwallaye 20 a waje a kaka guda ta La Liga.

Karin bayani