Wajibi ne a nada sabon kocin Ingila - Shearer

Alan Shearer
Image caption Alan Shearer ya taka rawa sosai a Ingila

Tsohon kyaftin din Ingila Alan Shearer ya ce wajibi ne hukumar kula da kwallon kafa ta Ingila FA ta nada sabon mai horas da 'yan kwallon kasar ba tare da bata lokaci ba.

Har yanzu Ingila ba ta da koci tun bayan da Fabio Capello ya yi murabus a watan Fabreru, inda kuma ake sa ran kocin Tottenham Harry Redknapp zai maye gurbinsa.

Ingila za ta yi atisayi kafin su tafi domin halartar gasar cin kofin kasashen Turai a ranar 6 ga watan Yuni.

"Suna bukatar koci ba tare da bata lokaci ba - koma kace yanzu-yanzun nan," kamar yadda ya shaida wa BBC Sports. Kamata ya yi FA ta maida hankali kan Ingila ba wai wasu kulob-kulob ba.

Shearer, wanda ya buga wasanni 34 a matsayin kyaftin ya zira kwallaye 30 a cikin wasanni 63, ya yi imani cewa Redknapp ne ya fi cancanta da aikin.

"Kasancewar Harry ya samu matsala a wasu wasanni hakan bai sa darajarsa ta ragu ba," a cewar tsohon dan wasan na Southampton da Blackburn da kuma Newcastle.

"FA na cikin tsaka mai wuya domin idan suka yi sakaci to mutane za su yi fushi da su".

Ita dai hukumar ta FA ta nace cewa za ta jira har sai "an kammala kakar bana" kafin ta bayyana wanda zai gaji Capello.