United ta lallasa Aston Villa da ci 4-0

United ta lallasa Aston Villa da ci 4-0
Image caption Manchester United ta baiwa Man City tazarar maki biyar

Manchester United ta karfafa matsayinta a saman teburin gasar Premier ta Ingila bayan da ta lallasa Atson Villa da ci 4-0.

Wayne Rooney ne ya zira kwallaye biyu yayin da Danny Welbeck da Nani suka ci daya-daya, a wasan da United din ta mamaye tun daga farko har zuwa karshe.

Wannan nasarar da United ta samu ta sa tazarar da ke tsakaninta da Manchester City ta koma maki biyar. City ta doke Norwich da ci 6-1 a ranar Asabar.

Tuni dai kocin Manchester City Roberto Mancini ya ce United ta riga ta lashe gasar ta Premier bana, amma kocin United Alex Ferguson ya ce har yanzu akwai sauran aiki.

Tun minti bakwai da fara wasan ne Rooney ya zira kwallon farko da bugun fanareti, sannan Danny Welback ya zira ta biyu a minti na 43.

Ana minti na 92 ne Nani wanda ya shigo wasan bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ya zira kwallo ta hudu.