Tshosane ya sabunta kwantiraginsa da Bostwana

Stanley Tshosane Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Stanley Tshosane ya taka rawar gani a Bostwana

Stanley Tshosane ya sabunta kwantiragi da shekaru uku domin ci gaba da kasancewa kocin 'yan kwallon Bostwana.

Shi ne ya jagoranci kasar a karon farko zuwa gasar cin kofin kasashen Afrika da aka yi a Equatorial Guinea da Gabona bana.

Tun da farko Tshosane ya yi watsi da kwantiragin da hukumar kula da kwallon kafa ta Bostwana ta yi masa tayi, yana mai kiran da a kara masa albashi.

Amma a yanzu an shawo kan wadannan matsaloli kuma Tshosane zai shirya domin tunkarar wasan share fage na gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya ta shekara ta 2014.

Za su fara wasansu na farko ne a rukunin A inda za su yi tattaki zuwa Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya a watan Yuni.

Bostwana ta sha kashi a dukkannin wasanni uku da ta buga a rukunin D a gasar ta cin kofin kasashen Afrika.