Wajibi ne Di Matteo ya lashe kofi - Ranieri

Roberto di Matteo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Roberto di Matteo ya samu nasara a wasanni tara daga cikin 12

Tsohon kocin Chelsea Claudio Ranieri ya ce idan Chelsea ta lashe kofin FA sannan ta kare a mataki na hudu a gasar Premier, to Roberto di Matteo na da damar ci gaba da kasancewa kocin kulob din.

Di Matteo ya samu nasara a wasanni tara daga cikin 12 da ya buga tun bayan da aka nadashi a matsayin kocin riko bayan da aka kori Andre Villas-Boas.

Da aka tambaye shi ko Di Matteo zai ci gaba da kasancewa a matsayin kocin Chelsea zuwa kakar badi, sai tsohon kocin ya ce: "Ya danganta.

"Idan ya lashe kofin FA kuma ya zo na hudu a Premier mai zai hana?"

Kocin dan kasar Italiya ya kara da cewa: "Roberto ya fara da kafar dama. Roberto ne ya fi cancanta ya yi abin arziki a can."

Ranieri, wanda ya jagoranci Chelsea daga shekara 2000 zuwa 2004, ya je Wembley ranar Lahadi domin kallon tsohon kulob din na sa a wasan da suka lallasa Tottenham da ci 5-1, inda a yanzu za su hadu da Liverpool.

Karin bayani