An sallamo Fabrice Muamba daga asibiti

Fabrice Muamba Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Muamba ya samu goyon baya daga sassan duniya daban-daban

Dan wasan Bolton Fabrice Muamba ya jinijinawa ma'aikatan asibitin London Chest Hospital bayan da aka sallame shi.

Dan wasan mai shekaru 24 ya yi "dogon suma" na sa'o'i 78 bayan da ya samu bugun zuciya a wasansu da Tottenham lokacin da yanke jiki ya fadi a ranar 17 ga watan Maris.

Tun daga lokacin ne dai ya ke kwance a asibiti.

"Hankali na ya kwanta da aka sallame ni daga asibiti," a cewarsa.

"Zan yi amfani da wannan damar wurin mika godiya ga dukkan ma'aikatan da suka taimaka wurin kula da lafiya ta."

A wata sanarwar hadin gwiwa da asibitin Barts Health NHS Trust da Bolton suka fitar, ya kara da cewa: "Juriya da kwarewarsu ta bani mamaki, don haka ba zan taba iya biyansu ba.

Ina kuma matukar mika godiya ga dukkan wadanda suka nuna goyon baya da fatan alheri a gare ni.

"A yanzu da aka salleme ni daga asibiti, zan mayar da hankali na wurin ci gaba da jinya da kuma zama tare da iyali na."

Kocin Bolton Wanderers Owen Coyle ya ce: "Hakika wannan labari ne mai dadin ji cewa an sallami Fabrice daga asibiti kuma kowa a kulob din yana cikin farin ciki.

Karin bayani