Zanga zanga ta kaure a shariar kwallon kafa ta Misra

Tashin hankali a Masar Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tashin hankali a Masar

An bude sharia kan masoya kwallon kafa da dama na kasar Masar a birnin Alkahira, cikin rudani.

Ana shariar ce kan zargin da ake wa mutanen da haddasa mummunan tashin hankalin da ba a taba ganin irin sa ba a kasar a lokacin wasan Al Ahly da Al Masri.

Mutanen da ake zargin wadanda cikin su har da yan sanda tara, sun kawo cikas ga zaman shariar, inda suka yi ta kururuwar bayyana rashin laifin su.

Ana zargin su ne da kisan gilla, da kuma nuna halin ko in kula a lokacin tashin hankalin.

Mutane dai a kalla 74 ne suka rasu sakamakon tashin hankalin da ya auku a Port Said, lokacin wasan da aka yi a ranar 1 ga watan Febrairun bana.