Karar Bin Hamman kan matakin FIFA za ta fara

FIFA Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption FIFA

A ranar Laraba ce ake sa ran kotu a kasar Switzerland za ta fara sauraren karar da tsohon dan takarar shugabancin hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA wato Mohamed bin Hammam ya shigar.

Shi dai Mohamed bin Hammam na kalubalantar dakatarwar sa ce ta tsawon rayuwa daga harkokin kwallon kafa da kotun FIFAr ta yi bisa zargin sa da cin hanci da rashawa a lokacin takarar sa da shugaban FIFAr Sepp Blatter.

Kotun ta ware kwanaki biyu domin duba shaidu kan balaguron da Bin Hammam ya yi zuwa Trinidad a watan Mayu na bara, lokacin yakin neman zaben sa.

Ana sa ran Bin Hammam ba zai halarci zaman kotun da za a yi a Lausanne ba, duk da jinjina wa kotun da ya yi, inda ya bayyana tsarin shariar FIFA da cewa ta jeka na yi ka ce.

Karin bayani