Ina son yin gudun da ban taba yi ba a Olympic, inji Bolt

Usain Bolt
Image caption Usain Bolt

Usain Bolt ya ce London 2012 za ta maida shi ya zamanto shahararren gwarzon dake raye.

Usain Bolt wanda ya samu zinari a gasar Olympic har sau ukku, na hankoron baiwa duniya mamaki a London 2012, inda yake sa ran gudun mita dari cikin dakikoki tara da digo hudu, sannan gudun mita dari biyu cikin dakikoki goma sha tara.

Bolt mai shekaru 25 a duniya dan kasar Jamaica, na cikin gaggan zakarun Olympic, kuma ya kafa tarihi a tseren mita dari cikin dakikoki tara da digo hamsin da takwas da kuma dakikoki 19 da digo 19 a tseren mita 200.

Usain Bolt ya ce mutane na son ganin na yi gudun dakiko 9 da digo 4 da kuma dakikoki 19.

Karin bayani