Tawagar yan wasan F1 sun tsallake rijiya da baya

Bahrain F1
Image caption Bahrain F1

Tawagar yan wasan India ta Force India, da suka je kasar Bahrain don halartar gasar tseren motoci ta Formula 1, sun tsallake rijiya da baya, akan hanyar su ta komawa masaukin su.

Makanikai hudu ne dake cikin wata motar Jeep suka gamu da wata arangama tsakanin yan sanda da masu zanga zangar adawa da gwamnati.

Yan sanda sun jefa hayaki mai sa hawaye wanda ya shiga cikin motar su, kafin daga bisani direban motar ya kusa ta surkukin hayaki ya bar wurin.

Babu wanda ya jikkata daga cikin su, amma an bukaci biyu daga cikin su da su koma gida.