Man U ce ta fi kudi a kwallon kafa, inji Forbes

manchester united
Image caption manchester united

Manchester United ce ta fi arziki a duniya cikin kulob din kwallon kafa, kamar yadda mujammal Forbes ta wallafa.

Nazarin mujallar ya nuna cewa, zakarun gasar Premiern su na da arzikin pam billion daya da million dari hudu, wanda ya sanya su na gaba cikin shekaru 8 a jere.

Real Madrid ce ta biyu, wadda aka kiyasta arzikin ta ya kai pan billion daya da million dari da dubu dari bakwai, yayin da Barcelona ke biye a matsayi na ukku, wadda ke da pan million dari takwas da goma sha shidda.

Mujallar Forbes ta ce magoya bayan Manchester United a duniya kusan million dari ukku da talatin sun taimaka wurin daukaka darajar kulob din a fagen kwallon kafa.

Karin bayani