Nadal ya doke Djokovic a gasar Monte Carlo

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rafael Nadal ya lashe gasar Monte Carlo a karo na takwas

Rafael Nadal ya lashe gasar Monte Carlo a karo na takwas a jere bayan da ya doke zakaran Tennis na daya a duniya Novak Djokovic da maki 6-3 da 6-1.

Nasarar da Nadal din ya samu shine na 42 da biyu a gasar ta Monte Carlo, amma wanan ne karo na farko da ya doke Djokovic bayan karawa takwas.

Bayan ya lashe wasan zagon farko, Nadal ya sha gaban Djokovic da maki hudu a wasa na biyu, kafin Djokovic din ya samu maki daya.

Gasar ta Monte Carlo Open a buga ta ne a kan laka a birnin Monaco da ke kasar Faransa.