Vettel ya lashe gasar Bahrain Grand Prix

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sebastian Vettel

Zakaran tseren motoci na Formula 1, Sebastian Vettel ya yi nasara a karon farko a shekarar 2012 inda ya yi gwagwarmaya da direban Lotus Kimi Raikkonen a gasar Bharain Grand Prix.

Vettel wanda ke tukawa kamfanin Red Bull mota, ya shiga gaba ne tun da aka fara tseren amma daga baya Kim wanda ya ke na goma sha daya ya kusan ya kamo shi bayan an kai rabin zagon tseren.

Vettel dai ya tsaya wasu gyare-gyaren wucin gadi, duk da cewa Raikkonen na kokarin ya kamo shi.

Direban Lotus Romain Grosjean ne ya zo na uku a tseren sanann direban McLaren Lewis Hamilton ya kammala tseren a matsayin na takwas.

Jenson Button dai bai samu ya kammala tseren ba, saboda wasu dalilai.

Direban Force India Paul di Resta, ya taka rawar gani a gasar inda ya kammala a matsayi na shida.