'Ban ga dalilin barin Real Madrid ba'- Mourinho

Image caption Kocin Real Madrid, Jose Mourinho

Kocin Real Madrid Jose Mourinho ya ce baya tunanin barin kungiyar a karshen kakar wasa na bana.

Real Madrid dai na gab da lashe gasar Laliga a Spaniya, wanda zai zama gasa na hudu kenan da Mourinho ya lashe a kasashe hudu.

Real dai na jagoranci ne a gasar Laliga da maki bakwai, amma akwai rahotanin da ke cewa Chelsea da Manchester City na zawarci Mourinho.

"A yanzu haka makoma ta bata da mahimmanci, amma ina ganin zan ci gaba da zama a kungiyar a kakar wasa na badi." In ji Mourinho.

"Ina da kwantaragi da kungiyar, kuma banga dalilin da zai sa in bar kungiyar ba."

Real Madrid dai ta nada Mourinho ne a matsayin kocin kungiyar a watan Mayun shekara ta 2010 na tsawon shekaru hudu.

Mourinho ya ce: "A karshen kakar wasa zan samu lokaci in tattauna da 'yan wasan da direktocin kungiyar sannan in yake shawara abun da ya fi mun alheri da kungiyar da kuma 'yan wasan."