Manchester United na zawarcin Eden Hazard

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Eden Hazzard

Kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson ya tabbatar da cewa kungiyar na zawarcin dan wasan Lille da Belgium Eden Hazard.

Ana dai alakanta dan wasan mai shekarun haihuwa 21 da kungiyoyi kamarsu Manchester City da Arsenal da Chelsea da kuma Tottenham.

Ferguson ya shaidawa wani gidan radio a Faransa cewa: "Na zo kallon wasan Lille da Lyon saboda inga yadda Hazard ke taka leda da kuma wasu 'yan wasa.

"Dan wasan kwararre ne, kuma yana sa sauri."