An tsananta hukunci a kan Al Masry

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Magoya kungiyar Al Masry

An tsananta hukuncin da aka dauka a kan kungiyar Al Masry a Masar, bayan tarzomar da ta barke a filin wasan kungiyar wanda ya sa aka yi asarar rayuka 74 a farkon wannan shekara.

A baya dai an dakatar da Kungiyar na tsawon wa'adin kakar wasa na bana amma yanzu an kara tsananta hukuncin da aka yiwa Kungiyar, yayinda idan ta dawo a kakar wasa na badi za ta buga ne a mataki na biyu saboda an rage mata matsayi.

Hukumar kwallon Masar ce ta tsananta hukuncin bayan ta sauri daukaka kara da aka yi game da batun a ranar Talata.

An dai daurawa magoya bayan kungiyar alhakin tayar da rikicin.

Kungiyar Al Ahly dai da farko ta fusata da hukunci da aka fara dauka a kan Masry.

Sama da mutane 70 ake tuhumu da hannu wajen rura rikicin da ya auku a wasan da Masry da Ahly su ka buga a ranar daya ga watan Fabrairu.