Mourinho na son Chelsea ta lashe gasar zakarun Turai

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jose Mourinho

Kocin Real Madrid, Jose Mourinho ya ce yana son Chelsea ta doke Bayern Munich a wasan karshe na gasar zakarun Turai, bayan da Bayern ta fidda Real a bugun fenarity a wasan kusa da na karshe.

Chelsea dai ta kai wasan karshe ne bayan ta doke Barcelona, duk da cewa dai ta buga wasa a Nou Camp ne na kusan sa'a guda da 'yan wasa goma.

"Ina mutakar son Chelsea ta yi nasara. Sun nuna jarumtaka yadda su ka doke Barcelona da 'yan wasa goma." In ji Mourinho.

"Ina alfahari da 'yan wasa na, dolene mu dauki kaddara."