Murray ya doke Giraldo a gasar Barcelona

Hakkin mallakar hoto AP

Dan wasa Tennis din Burtaniya, Andy Murray ya kai wasan gab da kusa da na karshe a gasar Barcelona Open baya ya doke dan Columbia Santiago Giraldo.

Murray ya doke Giraldo ne a wasa biyu da maki 6-1 da kuma 6-2.

Murray mai shekarun haihuwa 24 ya nuna bajinta a wasan a yayinda yake shirye-shirye halartar gasar French Open.

Murray zai fafata ne da Milos Raonic a wasan gab da kusa da na karshe a ranar Juma'a.

Shima dai Rafael Nadal ya kai wasan kusa da na karshe bayan ya doke Robert Farah da maki 6-2 da 6-3.