Chelsea ta Lallasa Rangers da ci 6-1

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Chelsea na murna

Chelsea ta lallasa Queens Park Rangers da ci shida da daya, inda dan wasannan Fernando Torres ya samu zura kwallo uku a ragar Rangers wato yayi hat trick.

A mintina ashirin da biyar ne dai Chelsea ta zura kwallaye hudu a ragar Rangers a zagaye na farko inda Torres ya ci biyu Daniel strurridge kuwa shine ya fara zura kwallon bayan an fara wasan da sakan arbain da biyar.

Torres ya kara ta biyar abunda ya sa yayi hat trick a wasan ke nan bayan da aka dawo zagaye na biyu.

Sai dai kuma Florent Malouda shima ya saka tasa ta shida kenan.

Daga bisani Djibril Cisse na Rangers, ya sa ka kwallo daya a ragar Chelsea inda aka tashi da ci shida da daya.

A wasan dai Torres yayi kaca kaca da bayan Rangers da dabarun nan nasa na a arta aguje a kuma saka kwallo.

Karin bayani