Harry ya ce Luka zai iya barin Tottenham

Hakkin mallakar hoto
Image caption Harry Redknapp

Manajan kulab din Tottenham, Harry Redknapp, ya fadi cewa dan wasannan Luka Modric zai iya barin kulab din a karshen kakar bana.

Labarin na zuwa ne kwana daya bayan da Winger Gareth Bale, 22, ya shaidawa BBc cewa zai bari matsawar kulab din ba su futo gasar cin kofin Champions League ba.

Redknapp ya ce kakar bara sun samu damar rike Luka, wanda acewarsa hakan na da mahimmanci, amma ya ce zai iya yin karya idan ya ce tabbas dan wasan zai tsaya a Tottenharm.

Modric mai shekara ashirin da shida, ya nuna kudirinsa na barin kulab din a shekara ta dubu biyu da goma sha daya amma kulab din yaki amincewa da tayin Pam miliyan arbain da Chelsea suka bayar a ranar karshe ta dibar yan

Karin bayani