Maria ta doke Azarenka a kwallon tennis

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Maria Sharapova

Maria Sharapova ta sa mu nasara kan Azarenka a gasar cin kofin kwallon Tennis na Stuttgart.

Maria, ta doke Azarenka wadda yanzu take rike da kambun duniya a Stuttgart.

Yan aksar Rashan dai ta ci 6-1 da kuma 6-4 inda hakan ya bata dada samun kambunta na ashirin da biyar ko da yake an doke ta har sau uku a wasannin karshe a shekara ta dubu biyu da goma sha biyu.

Azarenka ta doke ta a wasannin karshe na gasar Australia da India.

Azarenka wadda ta rasa kambu sau biyu wannan shekarar an warkar da ita wani ciwo da ta ji a hannunta a farkon zagaye na biyu na wasan.

Karin bayani