Podolski ya koma Arsenal

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Podolski

Lukas Podolski zai koma Arsenal daga Cologne a farkon kakar wassani mai zuwa.

Kawo yanzu dai ba'a fadi kudaden da aka sayi dan wasan mai shekaru ashirin da shida ba wanda ya fara wasa a Cologne ya koma Bayern Munich daga bisani kuma ya sake komawa shekarsa.

Podolski, ya ce yana matukar farin ciki da komawa Arsenal da kuma Premier League ya kara da cewa suna daga cikin manyan kulab da suke da tarihi a nahiyar Turai.

Manajan kulab din Arsenal, Arsene Wenger, ya bayyana Podolski a matsayin dan wasa na garari, mai cika aiki.

Karin bayani