Hodgson bai yi mamakin zama kocin ingila ba

Sabon kocin Ingila Roy Hodgson Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sabon kocin klub din kwallon kafa na Ingila, Roy Hodgson

Roy Hodgson yace bai yi mamaki ba game da zabensa da hukumar kwallon kafa ta Ingila ta yi don ya zama kocin klub din kwallon kafa na kasar.

Mutane da dama sun yi tsammanin Harry Redknapp ne zai maye gurbin Fabio Capello.

Shugaban hukumar kwallon kafar, David Bernstein ya bayyana cewa kwamitin mutane hudu da aka kafa don zaben sabon kocin ne suka yanke shawarar zaben Hudgson wata guda daya wuce.

Sai dai basu bada sanarwa game da hakan a hukunce ba, sai a ranar Lahadin da ta gabata.

Sam-sam ba a ma tuntubi kocin Tottenham ba wato Redknapp ba game da mukamin.

An kammala komai da komai game da kwantiragin shekaru hudu na Hodgson a Wembley ranar Talata.

Sabon kocin dai na tunkaho da cewa ayyukansa na baya ne suka sa ya fi dacewa da zama kocin klub din.