Tsohon dan bayannan Campbell yayi ritaya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sol Campbell

Tsohon rikakken dan bayannan na Ingila Sol Campbell, ya bada sanarwar ritayarsa daga wasan kwallon kafa bayan da ya shafe shekaru ashirin a fagen daga.

Tsohon dan wasan Arsenal, mai shekaru talatin da bakwai ba shi da kulab tun lokacin da kugiyar kwallon kafa ta Newcastle United ta sake shi a shekarar bara.

Sai dai Campbell a wata hira da akayi dashi yace abune mai wahala wanda ya yi fuce a wasa ya bari.

Karin bayani