Tommy Na ganin Moyes ne zai ga ji Ferguson

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption David Moyes

Tsohon kochiyan kulab din Manchester united, Tommy Docherty, ya yi hasashen cewa Sir Alex Ferguson zai nuna Kochiyan kulab din Everton ya zama magajinsa.

Tsohon mai bada horon na Manchester united, Docherty, ya yi amannar cewa zaa bawa Sir Alex Ferguson damar zabar wanda zai ga je shi inda ya ce yana ganin David Moyes zai nuna.

Sai dai an ambato Ferguson a watan Fabrairu na cewa yana son ci gaba da mukaminsa zuwa shekaru biyu ko ma uku.

Ferguson dai ya kusa ma yayi ritaya a shekara ta dubu biyu da biyu amma ya chanja raayi.

Karin bayani