Arsenal za ta ziyarci Najeriya a watan Agusta

Arsenal za ta ziyarci Najeriya a watan Agusta
Image caption Arsenal na da magoya baya sosai a Najeriya

Kungiyar Arsenal ta Ingila za ta ziyarci Abuja babban birnin Najeriya a ranar 5 ga watan Agusta mai zuwa domin buga wasannin sada zumunta.

A cewar wadanda suka shirya ziyarar, DanJan Sports, mai yiwuwa Arsenal za ta kara da daya daga cikin manyan kasashen nahiyar Afrika.

Wannan zai zamo karon farko da Arsenal za ta taka leda a Najeriya.

"Muna aiki wurin tantance wadanda Arsenal za ta kara dasu, kuma da zarar mun kamala za mu sanar da jama’a tare da kulob din," a cewar David Omigie na DanJan Sports.

"Najeriya ce tafi kowacce kasa yawan jama’a a nahiyar Afrika, kuma kungiyar da tafi kowacce yawan magoya baya a kasar za ta kai ziyara a watan Agusta."

“Wannan wata mafara ce ta wani babban lamari tsakanin kulob din da nahiyar Afrika.”

A jawabin da suka wallafa a shafinsu na internet, Arsenal ta ce: "Lokaci na karshe da Arsenal ta ziyarci Afrika shi ne a watan Yulin 1993, lokacin da suka je Afrika ta Kudu, kuma za ta koma sakamakon goyon bayan da take samu a Najeriya dama sauran sassan Afrika”.

Karin bayani