Redknapp ya saduda da zama kocin Ingila

Kocin Tottenham, Harry Redknapp
Image caption Kocin Tottenham, Harry Redknapp

Kocin Tottenham, Harry Redknapp yace ba zai taba jagorantar kungiyar kwallon kafa ta Ingila ba, bayan baiwa Roy Hodgson mukamin kocin.

Bayan nasarar da klub dinsa ya samu na ci hudu da daya akan klub din Bolton, Redknapp ya jaddada cewa baiyi da na sani ba duk da cewa mutane da dama sun so ya samu mukamin kocin Ingilan.

Redknapp dan shekaru 65 yace ya saduda a yanzu domin Roy na da shekaru hudu kuma yana masa fatn samun nasara.

Kocin yace yana farinciki da matsayinsa na yanzu kuma zai kara maida hankali yaga klub dinsa ya samu shiga gasar Champinions League.