Burtaniya ka iya kauracewa wasa a Ukraine

Hakkin mallakar hoto william hague
Image caption William Hague

Ministocin kasar Burtaniya za su iya kauracewa gasar wasannin tarayyar Turai na shekara ta dubu biyu da goma sha biyu da za'a yi a Ukraine don nuna rashin gamsuwarsu da yadda aka garke tsohuwar Prime Minsitar kasar Yulia Tymoshenko.

Ministan harkokin waje na Burtaniya, William Hague, ya shaidawa BBC cewa gwamnati na duba lamarin kuma za ta kai matsayar yanke hukunci kan ko Ministocin za su halarci gasar.

Sai dai shugabannin Turai da shugaban Hukumar Tarayyar turai Jose Manuel Barroso sun ce ba za su halarci wasanni a Ukraine ba.

Ms Tymosheko dai tana zaman kaso na wa'adin shekaru bakwai a gidan yari don zargin da akayi mata na rashin gudanar da aiyukan ofis yadda ya kamata.

Karin bayani