Roberto na da kwarin gwiwar zama Kochiya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Di Matteo na Chelsea

Kochiya mai rikon kwarya na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Roberto Di Matteo, yanzu bashi da fargabar zama cikakken kochiyan kulab din bayan da ya samu nasarar cin kofin FA bayan da kulab din ya ci Liverpool biyu da daya.

Matteo dai yayi wa Chelsea jagoranci zuwa wasan karshe na Champions League bayan da ya chanji Andre Villas Boas a watan Maris.

Di matteo wanda sau biyu aka taba cin kulab din a wasanni goma sha takwas tun da ya karbi jagorancin kulab din ya shaidawa BBC cewa yayi farin ciki da matsayinsa zuwa karshen wasannin kakar bana.

Dan Kasar Italiyan ya jin jinawa yan wasansa da irin nasarar da suka samu tun bayanda aka kori tsohon kochiyan Kulab din.

Karin bayani