Hague ya ce za a hana wasu shiga Birtaniya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Willian Hague

Ministan harkokin waje na Burtaniya, William Hague ya ce gwamnati ba za tayi kasa a gwiwa ba wajan amfani da ikonta kan sa ta kunkumin hana tafiya zuwa wasannin Olympics a London na 2012 ga mutane da ma wasu maaikata da suke da alaka da wasu gwamnatoci da ba a gamsu da mulkinsu ba.

Hague dai yaki amsa tambaya kan takamai man wadanda abun zai shafa amma ya bayyana a wata tattaunawa cewa ma'aikatan gasar cin kofin Olympics kamarsu General Mowaffak Joumaa na Syria da kuma Sheikh Nasser Bin Hamaad Al Khalifa na Bahrain za a duba su sosai kafin a basu izinin shiga Birtaniya don halartar wasannin Olympics.

General Joumaa, shugaban kwamitin wasannin olympics na Syria na da alaka da Shugaba Assad wanda Hague ya bayyana gwamnatinsa a matsayin mai aikata laifi kan murkushe masu adawa da gwamnati.

Karin bayani