Zambia na tabbatar da hukuncin FIFA

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'yan wasan Zambia

Hukumar kwallon kafa ta kasar Zambia ta shiga lamarin tabbatar da hukuncin da aka yankewa wasu yan wasa su tara kan hanasu wasa a duniya baki daya zuwa wani lokaci.

Duk yan wasan an same su da laifin karbar cin hanci a Finland shekarar da ta gabata inda aka yanke musu hukuncin hana buga wasa na tsawon shekaru biyu.

Hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA ta fadada hukuncin ya zama a duniya baki daya amma yan wasa biyu daga cikinsu Doewell Yobe da kuma Francis Kombe sun karya dokar inda suka buga wasa a Zambia.

Takunkumin da aka sawa Yobe na duniya baki daya anyi shi ne a ranar tara ga watan Janairu, shi kuwa Kombe ranar ashirin da uku ga watan Maris.

Karin bayani