Kociyan Ghana ya je bikon Gyan

Asamoah Gyan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Asamoah Gyan

Sabon mai horar da 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasar Ghana ya sauka a Hadaddiyar Daular Larabawa a yunkurinsa na sanya dan wasan Ghanan Asamoah Gyan ya sauya shawara kan dakatar da bugawa kasar sa wasa da yayi.

Shi dai kocin, Kwesi Appiah ya je kasar ne inda can Asamoa Gyan yake bugawa kulob din Al Ain wasa da zummar ya shawo kansa kan wannan mataki da ya dauka.

Hkan ya biyo bayan fushin da magoya bayan kungiyar su kayi dashi a kan bugun fenaretin da ya zubar abinda yayi sanadin fitar da kungiyar wasan ta Ghana a wasan kusa da na karshe na kofin kasashen Afrika.

A halin da ake ciki dai Asamoah ya bayyana aniyarsa ta dawowa bugawa kasar tasa wasa amma bai sanar da lokaci ba.