Hull City ta kori kocinta

Hakkin mallakar hoto Getty

Kulob din Hull city ya kori kocin sa, Nick Barmby kasa da watanni shida da fara aikinsa.

Tun a makon da ya gabata ne hukumar kulob din ta sanar da dakatar da shi akan wasu maganganu da yayi a kafafen yada labarai akan batun da ya shafi kudade na kungiyar.

Kalaman da Nick Barmby, din ya yi dai an ta'allaka su da cewa ya nuna hukumar kulob din ba ta bashi isassun kudade ba domin sayen 'yan wasa a lokacin musayar 'yan wasa a watan Janairu.

Wakilin BBC, David Burns wanda yace manajan kwararren matashi ne da ya hada 'yan wasa masu kyau yana ganin wasu da dama daga cikin 'yan wasan suma za su bar kulob din na Hull City, saboda sallamarsa da akayi.