Kocin Liverpool ya gamsu da kakar wasanni

Kocin klub din Liverpool, Kenny Dalglish Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kocin klub din Liverpool, Kenny Dalglish

Kocin klub din kwallon kafa na Liverpool Kenny Dalglish yace ya gamsu da wasannin da klub dinsa ya buga a kakar wasannin farko.

Ya bayyana hakan ne bayan nasarar da Liverpool ya samu akan klub din Chelsea.

Liverpool dai ta lashe gasar Carling, abinda ya sa klub din ya samu damar shiga gasar Europa kuma ya kaiga zagayen karshen na gasar cin kofin FA.

Sai dai klub din ya samu nasarar wasanni shida ne cikin wasanni 19 a gasar wasannin Premier a wannan kakar wasannin.

Wannan ne karo na biyu da Dalglish ya zamo kocin klub din bayan tafiyar tsohon kocin kulb din wato Roy Hodgson a watan Janairun shekarar 2011.

Inda ya sanya hannu a kwantiragin shekaru uku.