Fifa ta sanya Sierra Leone a gaban Najeriya

Hakkin mallakar hoto AFP

Kasar Afrika ta kudu ce tafi yunkurowa sama a sahun kasashen Afrika da su ka kware wajen taken leda da Fifa ta fitar a wannan wata.

Duk da cewa dai ba'a yi wasan kasa da kasa ba, tawagar Bafana Bafara ta daga sama zuwa mataki hudu inda a yanzu take na 67 a duniya.

A wani bangaren kuma, kasar Sierra Leone ce ta dago da mataki biyu, inda take na 61 a duniya a yayinda take saman Najeriya a karo na farko a tarihi.

Har yanzu dai kasar Ivory Coast ce ya daya a Afrika a yayinda kasar Ghana ke biye da ita.

Jamhuriyar demokradiyar Congo ce ta fi fuskantar koma baya a yayinda ta fado kasa da mataki biyar a yayinda tale ta 124 a duniya.

A duniya kuwa har yanzu kasar Spain ce ke ci gaba da jagoranci.