Hernandez ba zai buga a Olympics ba

Hakkin mallakar hoto Getty

Kungiyar Manchester United ta ce dan dan kasar Mexico, Javier Hernandez ba zai buga wasa ba a gasar Olympics din da za'a shirya a Landan.

A baya dai an zabi Hernandez a matsayin daya daga cikin 'yan wasan da shekarunsu ya wuce a gasar.

Amma kocin United, Sir Alex Ferguson ya shaidawa shafin kungiyar cewa; " Mun cimma yarjejeniya da hukumar kwallon Mexico cewa ya kamata a barshi ya huta."

Sai dai directan tawagar 'yan wasan Mexico Hector Gonzales ya ce Alex Ferguson ne ya hana dan wasan halartar gasar.

Hernandez, wanda zai cika shekaru 24 a ranar daya ga watan Yuni, zai takawa Mexico leda a wasan share fage na cin kofin duniya da kasar za ta buga da Guyana da kuma El-Salvador a farkon watan Yuni.