Mataimakin Wenger zai bar Arsenal

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kocin Arsenal, Arsene Wenger

Mataimakin koci a kungiyar Arsenal, Pat Rice zai bar kungiyar a karshen kakar wasa, kuma Steve Bould zai maye gurbinsa.

Rice, mai shekarun haihuwa 63, ya dade a mataimakin Arsene Wenger tun daga shekarar 1996.

"Ina son Pat ya yafe mun saboda 'yan matsalolin da mu ka fuskanta a baya, kuma a kullum ina goyon bayansa dari bisa dari.

"Pat gwarzo ne a Arsenal legend wanda ya sadaukarwa kungiyar rayuwarsa." In Wenger.