Yaya Toure na son taimakawa Man City

Hakkin mallakar hoto Reuters

Yaya Toure ya shaidawa BBC cewa yana son ya taimakawa Manchester City, ta zama babbar kungiya a duniya.

Dan wasan tsakiyan yana cikin yan wasan City da su ka taka rawar gani sosai a kungiyar, kuma akwai yiwuwar kungiyar ta lashe gasar Premier a karshen mako.

Ya ce: "Abun da yasa na zo kungiyar kenan domin in taimaka mata ta zama cikin sahun manyan kungiyoyi a duniya."

City za ta karbi bakuncin QPR ne a ranar Lahadi, kuma idan ta yi nasara za ta daga kofi.

Toure dai ya ce baya fuskantar matsin lamba, kuma ya jadadda cewa yana da kwarin gwiwa saboda a baya ya lashe wasu kofuna.

Toure, na cikin tawagar Barcelona ta lashe kafuna shida a kakar wasa ta 2009.