Tarihin Marigayi Rashidi Yekini

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

An haifi marigayi Rashidi Yekini ne a garin Kaduna dake arewacin Najeriya, a ranar 23 ga watan Oktober shekarar 1963.

Kuma tun yana da shekarun haihuwa 18 ya soma taka leda a babban mataki inda ya fara da kungiyar kwallon kafa ta UNTL dake garin Kaduna a shekarar 1981.

Bayan shekaru kusan biyu sai ya koma kungiyar Shooting Stars ta garin Badin wato jihar Oyo, daga nan kuma ya koma Abiola Babes daga shekarar 1984 zuwa 1987.

Rashidi Yekini ya tafi kasar Ivory Coast inda kungiyar Africa Sports ta siye shi don ya murza mata leda, kuma ya shafe shekaru uku a kasar kafin ya tsallaka turai a shekarar 1990 lokacin da kungiyar Victória Setúbal ta kasar Portugal ta siyeshi.

Kuma a kakar wasa ta shekarar 1993 zuwa 1994, Yekini ya kasance dan kwallon da yafi kowa cin kwallaye a gasar kwallon Portugal, inda zira kwallaye 34 cikin wasanni 32.

A shekarar 1994 kuwa, Rashidi Yekini ya koma kasar Girka ne da taka leda inda kungiyar Olympiacos ta siyeshi.

Daga nan kuma ya koma murza leda a gasar La Liga tare da Sporting Gijon amma bayan shekara guda sai ya kara komawa tsohuwar kungiyar ta Portugal wato Vitoria Setubal.

A shekarar 1997, Yekini ya koma FC Zurich ne a Switzerland.

A shekarar 1998 kuwa sai ya koma kwallonsa a kasar Tunisia tare da Athlétique Bizertin, daga nan kuma sai ya koma kungiyar Al-Shabab dake Riyadh a kasar Saudi Arabia.

A shekerar 1999 kuwa, angulu ce ta koma gidanta na tsamiya, saboda Rashidi Yekini ya kara komawa kungiyar ta Afrca Sports ne a Ivory Coast, kuma bayan karin wasu shekaru uku, sai ya dawo Najeriya inda ya bugawa kungiyoyin Julius Berger da kuma Gateway FC ta Abeokuta inda anan yayi ritaya a shekara ta 2005.

A bangaren Super Eagles kuwa, Rashidi Yekini ya zira kwallaye 37 a wasanni 58 da ya bugawa Najeriya, wanda kuma a tarihi har izuwa yanzu babu wani dan kwallon Najeriya da ya zira kwallaye masu yawan nasa.

Ya kuma halarci gasar cin kofin kwallon duniya sau biyu wato a Amurka a shekarar 1994 da kuma Faransa a shekarar 1998.

Har ila yau Rashidi Yekini ne ya ciwa Najeriya kwallonta na farko a gasar cin kofin duniya, wato kwallon daya zira a ragar Bulgaria, wanda a karshe Najeriya ta samu nasara daci uku.

Rashidi Yekini kuma ya halarci gasar cin kofin kwallon Afrika da dama hadda na shekarar 1994 a kasar Tunisia inda ya taimakawa Najeriya ta lashe gasar.

Abinda kuma yasa aka bashi gwarzon dan kwallon Afrika a wannan shekarar saboda irin namijin kokarin da yayi da kuma sadaukar da kai.

Sannan kuma ya bugawa Najeriya kwallo a gasar Olympics da aka yi a birnin Seoul a shekarar 1988.

Rashidi Yekini ya rasu a ranar Juma'a hudu ga wannan watan a garin Ibadan na jiyar Oyo dake kudancin Najeriya yana da shekaru 48 , kuma kafin rasuwarsa yayi fama da rashin lafiya.