Ferguson na fatan Man City ta yi sakaci

Sir Alex Ferguson Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Muna fatan City za ta yi wauta' -Sir Alex Ferguson

Kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson, ya ce yana fatan Manchetser City za ta aikata wata wauta wadda za ta baiwa kungiyarsa damar lashe Gasar Premier.

Ranar Lahadi Manchester City za ta karbi bakuncin QPR, tana kuma bukatar sakamako irin wanda United ta samu a wasanta da Sunderland ko ma wanda ya fi shi.

"Za mu yi iya kokarinmu mu yi nasara da fatan City za ta aikata wata wauta", in ji Ferguson.

Ya kuma kara da cewa City za ta yi fafutukar ganin ta ci wasanta ko ta halin kaka, amma kuma hakan kalubale ne a kanta.

"Sai dai kuma takaicin shan kashi a wasan ba zai misaltu ba. Ba za a iya kwatanta irin tasirin da hakan zai yi a kan kungiyar ba", in ji Ferguson.

Ya kuma bukaci 'yan wasan QPR su bayar da mamaki; QPR din dai na bukatar akalla maki daya don su ci gaba da kasancewa a Gasar Premier.

Karin bayani