Sabuwar jesin Liverpool ta jawo korafi

Hakkin mallakar hoto Liverpool FC

Kaddamar da sabuwar jesin Liverpool ta wasa a gida ya harzuka wasu daga cikin iyalan wadanda suka rasa rayukansu a hadarin gobarar da ya taba aukuwa a filin wasan Hillsborough.

A ranar juma'a ne aka kaddamar da sabuwar jesin ta kakar wasanninsu ta 2012-13 wadda wani kamfanin Amurka mai suna Warrior ya tsara.

Magoya bayan kungiyar sun yaba da yadda aka tsara rigar,amma hoton wutar da aka sa wanda ke alamta girmama wadanada suka rasu a harin wanda aka maida bayan rigar daga gabanta ya harzuka wasu da dama.

Hukumar kungiyar ta Liverpool ta ce ta yi kokari ta tuntubi iyalai bakwai na mamatan amma bata tuntubi wasu kungiyoyin da su ma suke rajin kare hakkin 'yan uwan mamatan ba akan wannan mataki da ta dauka na sake tsarin jesin.

Sai dai a wata sanarwa kungiyar masu kare hakkin wadanda hatsarin gobarar ya rutsa da su (HJC) a ranar 15 ga watan Afrilu 1989, kungiyar ta ce ta ga sanarwa ce kawai cewa ga abinda za ayi bayan an tuntubi iyalan mamatan.

Kungiyar tace yanzu tana da tabbacin cewa babu wani daga cikin iyalan mamatan da aka tuntuba akan lamarin kafin yanke wannan shawara.

Hukumar kungiyar ta Liverpool ta ce ta na bin lamarin da natsuwa ta kuma dauke shi da muhimmanci.

Karin bayani