City ta cancanci lashe Premier —Mancini

'Yan wasan Manchester City Hakkin mallakar hoto a
Image caption 'Yan wasan Manchester City suna murna bayan nasarar da suka yi a kan QPR

Kocin Manchester City, Roberto Mancini, ya ce kungiyar tasa ta cancanci lashe Gasar Premier bayan da ta kwace kofin ta hanyar lallasa Queenspark Rangers da ci uku da biyu.

City ta ci kwallaye biyu ne ana daf da tashi daga wasan, al'amarin da ya ba ta damar baiwa Manchester United mamaki da yawan kwallaye.

"Sau biyu muna lallasa Manchester United, mun ci kwallaye fiye da su, sannan kuma wasannin da muka sarayar ba su kai nasu yawa ba, saboda haka mun cancanci cin Gasar", in ji Mancini.

Ya kuma kara da cewa, "Ban taba karaya ba. An wahala kafin a kammala wasan da ma kakar wasannin, amma dai kungiyar da ta fi kwarewa ce ta yi nasarar lashe Gasar.

"Lokacin da na ce an riga an kammala Gasar a 'yan makwannin da suka wuce na fadi haka ne kawai saboda ina so in rage matsin lambar da ke kaina".

Mancini ya kuma ce yana matukar farin ciki saboda abin alfahari ne ga dukkan Italiyawa a ce dan Italiya ya lashe Gasar Premier ta Ingila.

City dai ta lashe wasanninta shida na karshe ne, ciki har da wasan da ta buga da makwabciyarta Newcastle a makwanni biyun da suka gabata, al'amarin da ya sa ta kamo United a yawan maki, yayinda United din ta yi ta tuntube.

Da haka ne City ta kwana da sanin cewa yin nasara a kan QPR ranar Lahadi zai ba ta kofin Gasar Premier a karo na farko tun shekarar 1968.

Karin bayani