Ferdinand-Zamu dawo da karfin mu

Dan wasan baya na kungiyar Manchester United, Rio Ferdinand, yace abokanan wasansa sun ji zafin yadda sukayi rashin nasarar daukar kofin Premier har makwabciyar su City ta dauka, amma zasu dawo da karfinsu a gasa ta gaba.

Ferdinand wanda sau biyar yana daukar kofin Premier da United din yace abin takaicine da ban haushi yadda suka yi rashin nasarar tsira da kofin a rana ta karshe.

''Dole ne mu tabbatar mun kara himma ....Kuma kada mu bari hakan ta sake faruwa'' inji Ferdinand.

Sai dai yace duk da sun rasa kofin Premier din lamarin da sauki tunda dai sun sami nasara a wasansu wanda hakan zai sa su kansu su tuna da yadda rashin nasara yake.

Karin bayani