Robin van Persie zai tattauna da Arsenal

Robin Van Persie Hakkin mallakar hoto
Image caption Robin Van Persie zai tattauna dangane da makomarsa a Arsenal

Dan wasan gaba Robin van Persie zai fara tattaunawa dangane da makomarsa a Arsenal yayin wata ganawa da kocin kungiyar, Arsene Wenger, da kuma shugabanta, Ivan Gazidis, ranar Laraba.

Ana sa ran fara tattaunawar a gidan Wenger da misalin karfe goma da rabi a agogon Burtaniya.

Sai dai zai yi wuya a cimma matsaya kafin Van Persie ya hade da tawagar 'yan wasan Holand ranar Alhamis.

Dan wasan mai shekaru ashirin da takwas da haihuwa, wanda ke da sauran shekara guda a kwantiraginsa, ya ci kwallaye arba'in da daya a wasanni hamsin da ukun da ya bugawa kungiyar ta Arsenal da ma kasarsa.

A cikin wannan adadi dai ya ci kwallaye talatin da bakwai ne a wasannin da ya bugawa kungiyar ta Arsenal guda arba'in da takwas; shi ne kuma dan wasan gaba mafi hazaka a Gasar Premier da kwallaye talatin a wasanni talatin da takwas.

Tuni dai wadansu manyan kungiyoyi suka nuna sha'awarsu ta sayen kyaftin din na Arsenal, wanda Kungiyar Kwararrun 'Yanwasan Kwallon Kafa da Kungiyar Marubuta Labarun Kwallon Kafa suka ayyana a matsayin gwarzon dan wasa na bana.

Karin bayani